Connect with us

Uncategorized

Fatima Aliko Dangote Ta Tallafawa Kungiyar Yan Jaridu Ta Arewa Online Journalist Forum Da Tallafin Shinkafa 

Published

on

Spread the love

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

Hajiya Fatima Aliko Dangote ta tallafawa Fitacciyar kungiyar yan jaridu ta (Arewa Online journalist Forum) da tallafin Shinkafa don rage raɗaɗi a watan Ramadan mai alfarma.

Hajiya Fatima tayi shura wajen ganin ta saka farin ciki a fuskokin Alummar Najeriya musamman arewacin Najeriya.

Advertisement

Mutum 8 Sun Shiga Hannu Kan Kisan Lakcara A Jami’ar UNIMAID

Hajiya Fatima ta kasance daya daga cikin jigo a kamfanin mahaifinta Dangote, ta biyo kalar kyawawan hali na mahaifinta Alhaji Aliko Dangote wajen ganin ta kyautatawa na kasa da ita

Shugaban Kungiyar yan jaridu ta (Arewa Online journalist Forum) Malam Barrah Almadany ya mika sakon godiya ga Uwar marayu Hajiya Fatima Aliko Dangote wajen yadda ta tsaya tsayin daka wajen tallafawa mabukata da kayan abinci a wannan wata na Ramadan.

Kazalika Almadany ya bukaci masu hannu da shinu suyi koyi da kalar halaye na Hajiya Fatima Aliko Dangote wajen taimakawa mabukata idan halin haka ya samu don rage raɗaɗi ga Yan kasa..

Advertisement
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply