Connect with us

News

Ƙarin Farashin Gas Ya Sanya Fargaba Akan Yiwuwar Kara Kuɗin Wutar Lantarki A Sassan Najeriya

Published

on

Spread the love

DAGA MARYAM BASHIR MUSA 

Matakin hukumar da ke kula da hada-hadar albarkatun man fetur na karin farashin gas ya sanya fargabar yiwuwar farashin wutar lantarki ya karu a sassan Najeriya, dai dai lokacin da hukumar lantarkin ke sanar da karuwar mutanen da ke amfani da mita.

Cikin wata sanarwar da hukumar ta fitar mai dauke da sa hannun shugabanta Farouk Ahmed ta bukaci kara farashin gas din da ake sayarwa kamfanonin rarraba wutar lantarki daga farashin dala 2 da centi 18 kan kowanne cubic zuwa dala 2 da centi 42.

Advertisement

Gwamnatin Jihar Zamfara Ta Haramta Zirga-zirga A Tsakanin Iyakokinta Da Katsina Da Sokoto Daga Karfe 7 Na Yamma

Radiyon Faransa ta ruwaito cewa sanarwar ta nemi kara farashin gas din da ake sayarwa daidaikun jama’a zuwa dala biyu da centi 92 daga dala 2 da centi 50 da ake sayarwa a baya.

A cewar Farouk, matakin da hukumar ta dauka ya yi dai dai da tanadin sashe na 167 na dokar masana’antar man fetur ta shekarar 2021 da ta sahale bibiyar farashin da kuma sauya shi lokaci zuwa lokaci da kuma banbanta farashin da ake sayarwa kamfanonin na lantarki da daidaikun jama’a.

Sai dai kuma tuni wannan mataki ya sanya fargabar yiwuwar hauhawar farashin lantarki a sassan Najeriyar dai dai lokacin da hukumar kula da lantarki ta kasar ke sanar da karuwar yawan masu amfani da mita zuwa mutum miliyan 12 da dubu 1 da 200.

Advertisement

Bisa al’ada idan har kamfanonin lantarki suka samu makamancin karin farashin gas din da suke tafiyar da harkokinsu da shi kai tsaye hakan na shafar daidaikun jama’a da kan sha wutar walau masu amfani da mita ko wadanda ake yankawa kudin wata-wata ba tare da mita ba.

Wannan mataki na zuwa ne a dai dai lokacin da mahukuntan Najeriyar ke shirin cire tallafin da gwamnati ke sanyawa a bangaren lantarki, lamarin da tuni ya sanya al’ummar kasar a fargaba lura da matsin rayuwar da ake fama da shi tun bayan cire tallafin man fetur.

Advertisement
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply