Connect with us

News

Ƴan Fansho A Kano Sun Buƙaci Hukumar EFCC Da Ta Kawo Musu Ɗauki

Published

on

Spread the love

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Ƴan fansho a jihar Kano sun bukaci hukumar kula da asusun fansho ta jihar ta hanzarta sayar da gidajen da hukumar EFCC ta karbo musu, wadanda gwamnatin jihar ke rike da su fiye da shekaru goma da suka gabata.

A shekara ta 2012 zuwa 2013 ne gwamnatin jihar Kano ta wancan lokaci ta ranci kudaden sama da naira miliyan dubu hudu daga asusun ‘yan fanshon jihar domin gina wasu rukunin gidaje bisa wani tsari na hada gwiwa domin saka jari.

Advertisement

Gwamnan Zamfara ya musanta ciyo bashin naira biliyan 14.26 da DMO ta wallafa

Tun da fari dai sai da wannan fasali ya fuskanci turjiya daga wani sashi na ‘yan fanshon jihar, amma da yake aikin ya gama, tilas ta sanya suka hakura.

Koda yake an gina gidajen a mashigar birnin Kano daga hanyar Zaria da kuma wasu akan titin zuwa Danbatta idan aka fito daga Kano, sai dai bayan wasu shekaru, wasu daga cikin ‘yan fanshon sun shigar da korafi gaban hukumar EFCC dangane da makomar kudaden da aka ranta daga asusun hukumar fanshon.

Bayan fiye da shekaru 10 wannan batu na gaban hukumar EFCC, a karshen wannan wata na Maris daya gabata ne hukumar ta EFCC ta mika takardun shaidar mallakar gidaje 324 ga Hukumar Kula da ‘Yan Fansho ta Kano bayan data karbo su daga hannun gwamnatin Kano wadanda kudin su ya kai naira miliyan dubu 4 da miliyan daya.

Advertisement

Wikki Time ta ruwaito cewa Kwamred Salisu Gwale shugaban kungiyar ‘yan fansho ta Najeriya reshen jihar Kano ya ce, “wadannan gidaje an kammala wasu wadansu kuma ba’a kammala su ba, kuma da aka tashi yin rabo sai akace mu ‘yan fansho za’a hada mana da wadanda ba’a kammala su, kuma a nan ne muka ki yarda, domin muna ganin ba dai-dai ba ne ace an dauki ruwan kudin mu anyi aiki dasu kuma a zo a ba mu gidajen da ba’a kammala su ba, hakan na daga cikin dalilan da suka haifar da takaddama tsawon shekaru har ta kai mu ga EFCC.”

Tuni dai Alhaji Habu Muhammad Fagge shugaban hukumar kula da asusun ‘yan fansho na jihar Kano ya tabbatar da karbar takardun wadancan gidaje.

Ya ce “Yanzu EFCC ta bamu takardun shaidar mallakar gidaje guda 324 bayan an yanke hukunci akan haka kuma zamu yi Nazari mu yi abin daya kamata bayan mun tattauna da dukkanin masu ruwa da tsaki akan wannan batu.”

Advertisement

 

Sai dai dangane da yadda ya kamata ayi da wadannan gidaje da hukumar EFCC ta yi nasarar kwatowa ‘yan fansho kuwa, Alhaji Salisu Gwale ya ce, “Mu muna bukatar hukumar ‘yan fansho ta jiha ta yi gaggawar sayar da wadannan gidaje domin a biya hakkin ‘yan fansho, saboda mutanen mu na cikin kuncin rayuwa sakamakon rashin samun hakkokin su na kammala aiki daga gwamnati na tsawon shekaru da dama”

Yanzu haka dai hukumar kula da asusun fansho ta jihar Kano na bin gwamnatin jihar bashin kudade sama da Naira biliyan 30, al’amarin da ya sanya galibin ma’aikatan jihar ke kwashe fiye da shekaru kafin su sami hakkokin su na sallama bayan ritaya daga aikin gwamnati.

Advertisement
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply